Gwamnan Kano ya haramtawa dalibai yin aikin wahala a makarantu

Abba Kabir Yusuf titun

Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi gargadi ga malaman makaranta, inda ya haramta musu saka dalibai yin aikin wahala tukuru, a filin makaranta da wajen makaranta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a ranar Lahadi.

Gwamnan ya jaddada cewa makarantu na ilimi ne da jagoranci na ɗabi’a ba na aikatau ba.

A wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai makarantar koyar da larabci da ke Kano, ya tarar da dalibai suna tono bututun bayan gida, inda a bayyane ya nuna rashin jin daɗi, tare da tambayar shugaban makarantar game da ba da irin waɗannan ayyuka ga ɗalibai.

Shugaban makarantar ya bayyana cewa an sanya aikin ne a wani bangare na koyon sa’o’i a makaranta, sai dai Yusuf ya ba da umarnin a daina wannan al’ada nan take.

Gwamnan ya tabbatarwa da mahukuntan makarantar cewa gwamnatinsa za ta gyara dukkan gine-ginen da suka lalace ciki har da masallaci.

Ya kuma ba da umarnin a mika duk wani aikin makaranta ga ma’aikatar ilimi ko ofishinsa domin aiwatar da shi.

Gwamna Yusuf, ya duba ayyukan sake gini da ake yi a maɗaba’ar jihar Kano, wanda aka lalata a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa.

Ya umurci dan kwangilar da ya bi kwangilar sosai, yana mai nuna damuwarsa kan yadda wasu gine-ginen ba su cika ka’idojin gwamnati ba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here