Dan majalisar da ke wakiltar Borno ta Kudu Sanata Ali Ndume, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta binciki ikirarin da dan majalisar dokokin Amurka Scott Perry ya yi na cewa hukumar ba da agaji ta Amurka USAID ta tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Ndume wanda tsohon shugaban kwamitin majalisar Dattawa kan Sojoji ne ya ce “Ba za ku iya cewa zargi ne kawai ba,” cikin shirin Siyasa a Lahadi na gidan talabijin na Channels
“Don haka ne ya sa gwamnatin Najeriya da majalisar dokoki ta kasa, musamman, ya kamata su duba zargin domin gudanar da bincike tare da tabbatar da sahihancin wannan babban zargi.”
Dan majalisar wanda ya shafe sama da shekaru 20 a majalisar dokokin kasar nan, ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta yi ruwa da tsaki a wannan batu na dan majalisar dokokin Amurka, duba da cewa an sha zargin cewa kungiyoyin agaji na kasashen waje da ke aiki a shiyyar Arewa maso Gabas mai fama da tashe-tashen hankula a Najeriyar na daukar nauyin ayyukan ta’addanci.
Labari mai alaka:Hukumar USAID ce ke tallafa wa Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci – dan majalisar dokokin Amurka
Ndume ya ce, “Wannan ci gaban yana da matukar tayar da hankali, musamman saboda daya daga cikin kungiyoyin ta’addancin da Scott Perry ya ambata, ita ce Boko Haram, kuma Boko Haram ta addabi yankin Arewa maso Gabas har ma da sauran sassan Najeriya.
“Za ku iya tunawa ‘yan Boko Haram sun kai harin bam a hedkwatar ‘yan sanda da ofishin majalisar dinkin Duniya da ke Abuja, kuma asarar da aka yi ta yi yawa, don haka dole ne gwamnatin ta yi bincike.
Ndume ya ci gaba da cewa, kamata ya yi Najeriya ta rika bayar da tallafin jin kai ga wasu kasashe ba wai su su rika bamu ba.