Dan majalisar dokokin Amurka Scott Perry, ya ce hukumar ba da agaji da raya kasashe ta Amurka USAID ce ke tallafa wa kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.
Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a yayin da ake gudanar da zaman taron kara wa juna sani na kwamitin inganta gwamnati a ranar Alhamis.
Perry ya kara da cewa hukumar ta USAID ta bayar da dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, yana mai zargin cewa har zuwa yanzu babu shaida na gina makarantun.
Karin karatu:Ƙasashen Amurka da Burtaniya sun ziyarci Najeriya don samun ingantacciyar kiwon lafiya – Pate
A baya dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira da a rufe hukumar ta USAID, inda ya zargi hukumar da cin hanci da rashawa a wani rubutu da ya wallafa a shafin internet.
Matakin wani bangare ne na yunkurin Trump da kuma hamshakin attajirinsa Elon Musk don dakile gwamnatin Amurka.
Musk, wanda Trump ya nada ya jagoranci ma’aikatar harkokin gwamnati, ya kuma soki hukumar ta USAID, yana mai zargin cewa tana gudanar da ayyukan damfara da tsattsauran ra’ayi kuma ya sha alwashin rufe ta.