Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da takwaransa na Jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, sun koma Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Sauya shekar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da rikicin cikin gida mai tsawo a jam’iyyar ADC, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce kan matakin siyasar da za su dauka.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa shugabannin biyu sun kammala komawa NDC ne a yayin wani muhimmin taron da aka gudanar a gidan shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson, da ke Abuja.
Taron ya hada su fuska-da-fuska da manyan jiga-jigan jam’iyyar a wani yunkuri da majiyoyi suka bayyana a matsayin wani bangare na shawarwari masu zurfi da nufin karfafa jam’iyyar.
An tarbi Kwankwaso da Obi da misalin ƙarfe 5:14 na yamma, daga nan aka fara tattaunawa da Dickson da sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Rahotanni sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan daidaita ra’ayoyi, tsarin jam’iyya, da kuma makomar siyasa.
Daga bisani aka ci gaba da tattaunawar a sirrance, wacce ta dauki sama da sa’a guda kafin a kammala da misalin ƙarfe 6:45 na yamma.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa a fadin kasa da su shiga NDC, yana mai jaddada bukatar hadin kai wajen gina jam’iyyar.
Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi jam’iyyar, yana gabatar da ita a matsayin wata madadin siyasa mai nagarta.
Obi, a nasa jawabin, ya yi gargadi ga ‘yan jam’iyya da su guji kai sabanin cikin gida kotu, maimakon haka ya yi kira da a bi hanyar tattaunawa da sulhu na cikin gida a matsayin hanya mafi dacewa ta dorewar hadin kai a cikin jam’iyyar.
Masu lura da al’amura na cewa shigowar wadannan mutane biyu babbar nasara ce ga NDC, duba da irin farin jinin da suke da shi da kuma kakkarfan tsarin da suke da shi a kasa, wani ci gaba da ka iya yin tasiri kan sabbin kawancen siyasa gabanin zabe masu zuwa.












































