Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a fadar sa dake Villa Abuja.
Shugaban kungiyar gwamnonin, gwamna Abubakar Bagudu ne ya jagoranci su zuwa taron, wanda aka yishi tsawun minti 30.
Wadan da suka halarci taron sun hada da Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagos, Dr Kayode Fayemi na Ekiti, Abubakar Badaru Jigawa, Dapo Abiodun Ogun, Abubakar Bello, Inuwa Yahaya, Abdullahi Sule da kuma mataimakin gwamnan jihar Deputy Ebonyi, Dr. Eric Igwe.
Har yanzo dai ba’a bayyanawa manema labarai dalilin taron ba, ko kuma abin da suka tau-tauna a gurin.










































