Man Utd ta doke Chelsea da ci 2-1

Manchester United

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta doke Chelsea da ci 2-1 a filin wasan ta na Old Trafford.

Nasarar da mai horar da ƙungiyar Ruben Amorim ya samu a ranar Asabar a gasar Firimiyar ƙasar ta Ingila za ta kasance babbar nasara a wannan lokaci da ƙungiyar ke fuskantar ƙalubale na rashin samun nasara a wasanni.

Ita kuwa Liverpool da ke saman teburin gasar ta Firimiya ta ci gaba da samun nasara bayan da ta doke Everton da ci 2-1 itama.

Sai dai mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham, Graham Potter na ci gaba da samun matsi a kakar baya, biyo bayan rashin nasara da ya yi a wasanni 4 cikin 5 a Jere wanda hakan yasa ƙungiyar yanzu haka ke cikin ƙungiyoyin da za su faɗa rukuni na biyu na gasar Firemiya “Religesion” idan suka kare a kasan tebur a kakar wasannin da ake yi.

Kafin fara zura ƙwallo a wasan da United din ta samu nasarar dai mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea Robert Sanchez ya samu katin kora wato Jankati daga alkalin wasa.

Hakan yasa a minti na 14 kyaftin din ƙungiyar ta United Bruno Fernandes ya zura kwallo a ragar Chelsea.

Sai kuma ɗan wasa Casemiro ya zura kwallo ta 2 a mintuna na 37 sai dai shi kansa dan wasa Casmiro ya samu katin na Kora bayan da ya samu yalon kati sau biyu a wasan, hakan yasa kowacce kungiya ta ƙarƙare wasan da yan wasa 10.

Sai dai ɗan wasan Chelsea Trevoh Chalobah ya warware ƙwallo daya kafin tashi daga wasan da ƙungiyar ta United ta sanya musu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here