Gasar cin kofin Duniya: Kocin Saudiyya ya musanta baiwa ‘yan wasan kyautar mota kirar Rolls Royce

Saudi coach denies Rolls Royce gifts for team
Saudi coach denies Rolls Royce gifts for team

Mai Horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Saudiyya Herve Renard, ya ce rahotannin da ke cewa yarima mai jiran gado, Mohammed bn Salman, zai bai wa daukacin tawagarsa kyautar mota kirar Rolls Royce kan nasarar da suka yi da Argentina ba kamshin gaskiya.

Awani rahoto da jaridar New York Post ta fitar, tace kocin ya ce babu kanshin gaskiya kan rahoton.

Renard ya ce, “Babu wani gaskiya game da wannan rahotannin, muna matakan tarayya da ma’aikatar wasanni kuma ba lokacin da za a samu wani abu bane yanzu.

Wasa daya kawai muka buga, muna da wasanni biyu masu matukar muhimmanci [matakin rukuni] kuma muna fatan samun nasara a wasu.”

Abinda kawai ke da kyau a ƙarshen wannan rukunin rukuni shine mu zamo na 1 ko na 2.” in ji Renard.

Shi ma Saleh al-Shehri wanda ke buga gaba a kungiyar ta Saudiyya ya tabbatar da cewa rahoton karya ne. “Ba gaskiya ba ne, mun zo nan ne don hidimtawa kasarmu kuma mu yi iya kokarinmu.

Jaridar New York Post ta bada rahoton cewa, da’awar ta fito ne daga shafin twitter na wani likitan hakori dan Pakistan wanda ba shi da masaniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here