Hedikwatar tsaro ta tabbatar da hallaka Manyan Kwamandojin ‘Yan Ta’adda

nigerian army training
nigerian army training

Hedikwatar tsaro ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ‘yan ta’adda hudu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.

Kwamandojin sun hadar da Machika da Haro da Dan Muhammadu sai Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje.

Daraktan yada labaran sojojin, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Buba yace Machika kwararren mai hada bama-bamai ne kuma kanin fitaccen dan ta’adda (Dogo Gide) ne.

Yayin da Haro da Dan Muhammadu suka kware a harkar garkuwa da mutane.

Karanta wannan: Hukumar NDLEA ta kama wanda ake zargi da kashe jami’inta a Sokoto

Ya ce wani farmakin hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai a ranar 11 ga watan Disamba, sun kashe Kachalla Kawaje.

Ya kara da cewa an kashe Kachalla ne a karamar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu dakaru dake tare da shi.

Sojojin Najeriya

Acewar Buba harin da aka kai ya yi sanadin kashe kwamandojin ‘yan ta’adda sama da 38 yayin da aka kama wasu 159.

Buba ya ce, a yankin Kudu maso Gabas ma, sojoji tare da wasu jami’an tsaro sun kama kwamandan haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafra masu dauke da makamai.

Yan ta'adda
Yan ta’adda

Yace an kama Uchechukwu Akpa ne, tare da wasu kananan kwamandoji uku, wato Udoka Anthony Ude da Ikechukwu Ulanta da kuma Ezennaya Udeigewere.

A cewarsa, an kama mutanen uku ne bayan wani samame da aka kai maboyarsu a cocin King Catholic Church dake Ameta Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Buba ya ce sojojin da ke yankin Neja Delta sun lalata ramuka 15 da  kwale-kwale 25 da tankunan ajiya 74 da motoci 14 da tukwanen dafa abinci 115.

Sauran abubuwan sun hada da mazubin ruwa 13 da na’urorin sanyaya daki 10 da sauran kayayyaki.

Yace sojojin sun kwato lita dubu 357 da 350 na danyen mai da aka sace da lita dubu 185 da 300 na tataccen mai da kuma lita dubu 20 da 600 na gurbataccen mai.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here