Daliban jami’ar FUDMA da aka yi garkuwa da su sun shaki iskar yanci

FUDMA New
FUDMA New

Hukumar jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma a jihar Katsina, ta tabbatar da kubutar sauran Daliban jami’ar Mata dake hannun masu garkuwa.

Shugaban jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai ranar juma’a a Katsina.

Yace dalibai matan da suka shaki iskar yancin wasu ne daga cikin Dalibai biyar da aka yi garkuwa da su a baya.

Karanta wanannan: Hedikwatar tsaro ta tabbatar da hallaka Manyan Kwamandojin ‘Yan Ta’adda

Tun a ranar 3 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka yi garkuwa da daliban a gidan da suke haya dake kusa makarantar Mariyamu Ajiri memorial, dake Dutsinma.

Hamisu yace yanzu haka za’a duba lafiyar su kafin damka su a hannun iyalan su.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya tuna cewa tun a ranar 3 ga watan Oktoban shekarar 2023, ‘yan sanda suka tabbatar da yin garkuwa da ‘yan matan.

Kazalika a ranar 20 ga watan Nuwambar da ya gabata ‘yan sandan suka tabbatar da kubutar daya daga cikin daliban dakd hannun masu garkuwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here