Wani dalibin jami’ar tarayya ta Kashere dake Gombe, Abdussamad Musa, ya rasa rayuwar sa sakamakon musun ball da barke tsakanin sa da abokan sa.
Dalibin dake aji biyu a jami’ar ya mutune sakamakon caka masa wuka a wuya da abokan sa sukai a cikin jami’ar.
A cewar shaidun gani da ido, rikicin ya faro ne tun da sanyin safiyar Laraba.
Wani abokin marigayin mai suna Aliyu Usman, na sashen koyar da kimiyyar siyasa a jami’ar yace an kashe dalibin ne biyo bayan zazzafan musun ball daya barki tsakanin murgayin da abokan sa.
“Musun kwallon kafa ne yaja wlh, kusan bayan gama musun ma kowa ya watse, da rabon dai sai hakan ta faru, shi abokin namu bai bar gurin ba, sai akai tahu mugama dashi, inda hakan yaja aka caka masa wuka a wuya”
Majalisar Wakilan Dalibai ta Jami’ar (SRC) ta yi Allah wadai da faruwar lamarin, ta kuma sha alwashin ganin anyi adalci, tare da hada kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata laifin.
Shugaban SRC Abdulra’uf Auwal ya ce “Mun himmatu wajen ganin an gurfanar da wadanda suka aikata lefin”
“A halin yanzu abun yana hannun jami’an tsaro, kuma za mu bi diddigi domin ganin anyi adalci.”
Shugaban jami’an tsaro na jami’ar, Mukhtar Zailani, ya tabbatar da cewa an kama wadanda ake zargi da aikata lefin.
Wadanda suka hada da shugaban kungiyar Iliya Mshelia da karin wasu mutane 13.
Ya kuma kara da cewa yanzu haka wadanda ake zargin suna hannun yan sandan jihar Gombe.