Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kalubalanci karars da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar domin hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.
Jonathan, ta hannun lauyansa, Chief Chris Uche, SAN, ya shigar da karar farko don jalubalantar karar da Jideobi ya shigar, inda ya roki Alkalin Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a Peter Lifu, da ya soke karar saboda rashin hurumin kotun.
A cewar tsohon shugaban kasan, karar tsantsar hasashe ce, wacce aka gina kan zato, wacce ta yi gaggawa kuma ta dogara ne kan hasashen kafofin watsa labarai, domin babu zabe, babu takara, kuma babu wani dalilin kara da ta taso.










































