Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’i ya koka kan ƙarancin fitowar masu zabe da aka fuskanta a jihar.
Tun da sanyin safiya ne dai ma’aikatan zaɓe suka isa rumfunan zaɓen a kan lokaci tare da tabbatar da kayan aikinsu sun zama cikin shiri.
Da misalin karfe tawkas na safiya ne dai aka fara zaben, shi ma gwamnan jihar ya isa inda zai yi zaɓe da misalin karfe tara na safiyar, sai dai kai tsaye ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya shaida wa idanunsa na ƙarancin masu zaben.
‘‘Dole a jinjinawa INEC, abubuwa sun yi sauki sosai kuma ni ban samu matsala ba da zaɓena ba.
‘‘Abin da na fuskanta shi ne mutane da dama ba su fito ba, wanda wannan abu ne mara daɗi, amma ina kira ga jama’a da su fito su kaɗa ƙuri’unsu.
‘‘Yawan kuri’armu yana nuni da karfin da muke da shi, kuma babu abin da zamu ce sai son barka,“ in ji El Rufa’i.










































