NDLEA ta kama wakilan jam’iyya da katunan cirar kuɗi ‘na sayen ƙuri’a’

1679144249292
1679144249292

Jami’an hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wasu mutum huɗu da ɗaruruwan katunan cirar kuɗi domin sayen ƙuri’a a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an loda wa kowanne kati naira 10,000, tare da saka masa lambobin sirri, waɗanda ake zargin na sayen ƙuri’a ne.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here