Fitaccen malamin addinin musulunci a Zaria, Sheikh Usman Idris Kusfa, wanda aka fi sani da Rigi-Rigi, ya rasu yana da shekara 57 a duniya.
Babban almajirinsa Malam Nasiruddeen Umar Baharu ne ya sanar da rasuwarsa ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a ranar Litinin a Zaria.
Sheikh Usman Kusfa ya rasu ne da sanyin safiyar Litinin a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kaduna, bayan ya shafe watanni yana fama da jinya.
Marigayin ya shahara sosai wajen koyarwar addinin musulunci, kuma ya samu karɓuwa matuƙa a kafafen sada zumunta na zamani kamar TikTok da sauran hanyoyin sadarwa na zamani.
Sheikh Kusfa ya bar mata huɗu, da ’ya’ya 37, tare da jikoki masu yawa.
An tsara gudanar da sallar jana’izarsa a Kusfa cikin birnin Zaria da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma a ranar Litinin.
NAN













































