Faisal Sanusi, matashi ne mai shekaru 27, wanda aka fi sanin shi da Faisal-Art dake unguwar Koki, karamar hukumar Dala a jihar Kano.
A cikin hirar mu da yai da Jaridar SOLACEBASE ya fadi yadda ya kera kera babur mai kafa uku cikin shekara daya.
Ko zamu iya jin sunan ka dakuma matakin karatun ka?
Sunana Faisal Sanusi kuma an haife ni a shekarar 1995 a unguwar Koki dake karamar hukumar Dala a Kano, Yanzu haka inada shakara 27.

Na yi makarantar firamare a Dantata Memoria Day Pramary School, bayan na kammala firamare na wuce makarantar gwamnati dake Gwammaja a karamar hukumar Dala a jihar kano.
Anan na kammala sakandare kuma daga nan banyi wani yunkurin shiga jami’a ba har zuwa yanzu.
Shin ko kanada niyyar ci gaba da karatu don samun ƙarin ilimin fasaha?
Gaskiya a yanzu dai banida halin zuwa jami’a. Ina gudanar da bincike na don samun karin ilimi ta hanyar amfani da yanar gizo. Ko da yake ba zan iya yanke hukunci kan yiwuwar cigaba da karantu ba, wala-alla nan gaba idan na sami kudi zan iya komawa makaranta.

Me za ka iya fadama game da ƙirƙirar babur mai kafa uku , ina nufin ta yaya ka fara tun amatakin farko?
To, kafin kirkiro wannan Keken, nayi kere-kere da dama, kamar kafar keken dinki, injina da wasu kananan na’urori da yawa a gida. Wannan ne kawai ya fi daukar hankali saboda fasahar tafi burge mutane.
Da farko kaga mota naso na kera amma saboda rashin wasu kayan aiki sai na yanke shawarar na fara da ‘Keke Napep’ amma duk da haka nan gaba kadan zan kera mota ta Insha Allahu.

Babu wanda ya koya mini komai a wannan aikin. Tun da farko, na fara da zana shi a takarda, sannan na tsara zanen ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa.
Galibi kayan aikin da na yi amfani da su, ni na har-hada su. Na sayi injin walda kuma na koyi yadda ake sarrafa shi. Ban je wurin kowa don a koyan yadda ake sarrafa shi ba. Duk abin da kake iya gani a wannan babur din ni na haɗa su ni kaɗai ba tare da zuwa wurin kowa ba. Na gode wa Allah da ya bani baiwar yin hakan.
Na fara aikin a shekarar bara. Ko da yake ban wani maida hankali sosai ba, da kuwa na maida hankali bazai kai shekara ba, zan gama hada shi.
Ta yaya ka samo kayan hada shi da sauran abubuwa yayin ƙirƙirar keken, Shin ka sami tallafin kuɗi ne?
Gaskiya, ban samu ba. Ina amfani da ɗan abin nake dashi daga irin kasuwancin danake yi na saye da sayarwa.

Me ya baka kwarin gwiwa yin wannan sabon samfurin keke me kafa uku?
Tom, tun lokacin danake ƙarami, an ƙarfafa min a fannin ƙirƙire – ƙirƙire. Yayin da na zama matashi, ina alfahari da abin danayi ya burge mutane, Kuma ina kokari dan sauƙaƙa ƙalubalen zamantakewar jama’a akan sufuri.

Nawa ne adadin kudin da ka kashe wajan kera wannan keken?
Kamar yadda na fada muku, ban sami wani tallafi ba. Zan iya cewa na kashe kusan Naira dubu dari shida (600,000) yayin hada wannan keken. Sannan kuma babur din yana iya daukar lita hudu na man fetur, kwatankwacin irin yadda na kasashen waje ke iya daukar lita 4.
Yaya kake tunanin ganin kan ka a nan gaba?
Babban burina shine in kafa kamfanin masana’antu wata rana. Ƙirƙirar wannan keken mai kafa uku shine mafari. Duk da ba don kasuwanci na samar dashi ba, amma ina tunanin wata rana zan kafa kamfanin kera babura da motoci da makamantansu har ma da jiragen sama.

Yanzu ace gwamnatin tarayya ko ta jiha ko wata kungiya nason tallafawa shirin ka, Shin zakayi maraba da shi?
Eh, tabbas ina maraba da shi, idan har zan iya samun tallafin daga koma waye, ya-alla gwamnati ko kungiyoyi masu zaman kansu. Zan cigaba da amfani da ɗan abin da nake da shi har izuwa lokacin da Allah zai tabbatar da mafarkina likafa ta tayi gaba.

Wanne kira zaka yi ga matasa?
To, kirana ga matasa shi ne kada su tsaya sanya ko jiran gawon shanu don fara aiwatar da wata fasaha dasu ke da ita. Akwai matasa da yawa da suke da fasahar kirkire-kirkire amma ba sa gwada fasahar ta su.













































