Karamar hukumar Madobi ta gudanar bitar kiwon lapia mata masu juna biyu da kananun yara karo na 7

IMG 20221008 WA0024
IMG 20221008 WA0024

Majalisar karamar hukumar Madobi ta jaddada kudirin ta na cigaba da kulada harkokin kiwon lafiya musamman mata masu juna biyu da kananun yara.

Shugaban Ma’aikata na karamar hukumar Alh. Auwal Sunusi Gora ya bayyana haka yayin gangamin wayarda kan mata muhimmancin kulada kiwon lapia dakuma yunkurin da karamar hukumar keyi na inganta walwalar al’ummar yankin.

Alh Auwal Gora ya nuna farin ciki gameda yunkuri da Uwargidan Shugaban karamar hukumar keyi na fadakar da mata muhimmancin kulada kiwon lapia tareda tattaki zuwa mazabu 12 na yankin dan fadakar dasu.

Yace gangamin na yau a mazabar GORA, ita ce maza6a ta 7 acigaba da rangadin da ayarin Uwargidan Shugaban karamar hukumar ke kaiwa mazabun yankin dan wayarda kan mata.

Ajawaban da ta gabatar tun da farko, Me Masaukin baki, kuma Uwargidan Shugaban karamar hukumar Hajia Maryam Lawan Yahaya ta ce
karamar hukumar ta himmatu wajan kulada kiwon lapiyar mata masu juna biyu da kananun yara dakuma
samarda gyadar yara a kananu da manyan asibitoci dake yankin.

Hajia Maryam Lawan Yahaya ta nanata kudirin karamar hukumar na cigaba baiwa kiwon lapia fifiko dakuma fadakar da mata ilimin kulada lafiyar jarirai da kananun yara tareda alwashin cigaba da fito da irin kokarin da karamar hukumar keyi na kulawa da mata a matsayin su na iyayen kasa.

A tsokacin da ta gabatar, Uwargidan tsohon kwamishinan raya karkara da birane Hajia Zainab Musa iliyasu kwankwaso ta yaba bisa yadda dandazon matan suka amsa kira tareda nuna jin dadi gameda ayyukan da karamar hukumar take musu.

Zainab kwankwaso ta bayyana jin dadi tareda kira ga matan dasu cigaba da bada hadin kai musamman a zabukan dake tafe, dan samun cigaba da kulawa dasu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here