Ambaliyar kogin lokoja, Rashin ingantattun hanyoyi ya kawo karancin man fetir a Abuja

IMG 20221008 WA0023
IMG 20221008 WA0023

Kungiyar dillalan man fetur  dake jigilar rarraba man ta ce karancin man fetur da ake fuskanta a yanzu haka a babban birnin tarayya Abuja na da alaka da ambaliyar ruwa a Koton-Karfe da ke jihar Kogi.

Koton Karfe dai wata al’umma ce dake tsakanin babban birnin tarayya Abuja da Lokoja inda ambaliyar ruwa ta tafka mummunar barna a baya-bayan nan.

Ambaliyar ruwan da ta afku a yankin ta mamaye mafi yawan yankunan Koton Karfe da Lokoja tare da hana zirga-zirgar ababen hawa.

Kungiyar ta kuma alakanta karancin hanyoyin da za a bi zuwa babban birnin tarayya Abuja dasuka lalace tare da ramuka ke bada wuya wajen wucewa zuwa birnin Abuja.

Kungiyar ta ce lamarin ya mauda hannun agogo baya, inda ta bukaci ma’aikatar ayyuka da gidaje da hukumar kula da tituna ta tarayya da su kawo dauki dan warware matsalar.

Shugaban kungiyar dillalan dakon, Alhaji Lawan Dan-Zaki, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja cewa, mafita ita ce a gaggauta sake gina hanyar Lambata-Lapai-Agaie-Bida da ta lalace a jihar Neja wadda ta zama karfen-kafa ga matafiya.

Dan-Zaki ya kuma koka da irin takaicin da direbobin manyan motocin dakon man fetur ke fuskanta a fadin kasar nan, inda direbobin manyan motoci kan kaucewa hanyar Mokwa zuwa Kaduna saboda rashin tsaro, inda ta nan ne ake garkuwa da direbobi a wannan hanya.

Da yake mayar da jawabi kan wannan tirka tirkaci Babban Konturola na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya a Neja          Mista Moshood Samotu ya ce ana ci gaba da aiki a hanyar Lambata-Lapai-Agaie zuwa Bida.

Ya ce anci kimanin kashi 51 cikin 100 na aikin sake gina hanyar Lambata-Lapai-Agaie-Bida aka gama aiwatar wa  a watan Satumba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here