Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya rasu.

PDP PDP 1 1
PDP PDP 1 1

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kkas Cif Vincent Ogbulafor ya rasu.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa jaridar Solacebase rasuwar Ogbulafor.

Majiyar ta ce tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya rasu ne a kasar Canada yana da shekaru 73 a duniya sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Ogbulafor wanda ya fito daga yankin Olokoro na karamar hukumar Umuahia ta Kudu a jihar Abia.

An haife shi ne a ranar 24 gawatan Mayu 1949, kuma ya rasu a daren ranar Alhamis” in ji majiyar iyalan sa.

Ogbulafor ya kasance sakataren jam’iyyar PDP na kasa na farko kafin daga bisani ya zama shugaban jam’iyyar na kasa bayan kazamin fadan da ya barke tsakanin Sanata Sam Egwu da Sanata Anyim Pius Anyim.

Daga baya dai bayan tirka-tirkar aka tilasta masa yin murabus a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Tsohon gwamnan jihar Enugu Dr. Okwesilieze Nwodo ne ya gaje shi a matsayin shugaban jam’iyyar amatakin kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here