An kama gawurtaccen mai fataucin miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo bayan shekaru 12 ana zarginsa da kashe jami’an NDLEA uku

imgonline com ua twotoone OogFFF83uKjn7sX3 1 1 750x430

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA sun kama wani fitaccen jagoran mafataucin miyagun ƙwayoyi mai suna Lekan Jimoh, wanda aka fi sani da Kanmo-kanmo, bayan shafe shekaru 12 ana nemansa bisa zargin jagorantar kisan jami’an NDLEA uku.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an gano Kanmo-kanmo a maboyarsa da ke garin Owode a Jihar Ogun, inda ƙungiyoyin sintiri na hukumar suka kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri, lamarin da ya kawo ƙarshen dogon binciken da aka dade ana yi masa.

A yayin samamen, jami’an NDLEA sun samu kilogiram 69 na skunk, wani nau’in tabar wiwi, a hannun wanda ake zargin, tare da tabbatar da cewa yana da tarihin gujewa kame da kuma shirya kai hare-hare ta hanyar amfani da ‘yan daba masu makamai kan jami’an tsaro.

Karanta: Da ɗumi-ɗumi: Ƴan sanda sun cafke mutane 3 da ake zargi da kisan Uwar da yara 6 a Kano

Bincike ya nuna cewa a wani lamari a baya, Lekan Jimoh ya jagoranci taron tarzoma a kan jami’an NDLEA da suka yi yunkurin kama shi, wanda ya kai ga kisan jami’ai uku, ciki har da Rabiu Usman Kazaure, kafin ya tsere daga wurin, yayin da hukumar ta ci gaba da bibiyarsa tsawon lokaci.

A wani samame na daban a baya, jami’an NDLEA sun kwato buhuna 139 na skunk masu nauyin fiye da tan 1,900 daga wani gidansa da ke Ado-Odo a Jihar Ogun, inda daga baya kotu ta ƙwace gidan tare da mika shi ga gwamnatin tarayya saboda amfani da shi wajen ajiye miyagun ƙwayoyi.

A halin yanzu, hukumar NDLEA ta ci gaba da kai samame a jihohi daban-daban na ƙasar, inda aka kama wasu masu fataucin miyagun ƙwayoyi tare da kwato manyan adadin kwayoyi da magunguna.

Tuni dai hugabancin hukumar ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan tare da jaddada kudirin ganin an tabbatar da adalci ga duk wanda ya aikata laifi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here