Kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta bayar da umarnin tsare Yakubu Adamu, kwamishinan kudi na Jihar Bauchi, yayin da take jiran yanke hukunci kan bukatar belinsa.
Alkalin kotun, Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ne bayan lauyan Adamu ya gabatar da bukatar beli, inda lauyan hukumar EFCC ya nuna adawa da bukatar.
Lamarin ya biyo bayan gurfanar da Yakubu Adamu tare da kamfanin Ayab Agro Products and Freight Company Ltd a gaban kotu bisa tuhume-tuhume guda shida da suka shafi zargin badaƙalar kudade har kimanin N4.6bn.
Hukumar EFCC ta sanya sunan Adamu da kamfanin a matsayin wadanda ake tuhuma na farko da na biyu a karar da ta shigar.
Labari mai alaƙa: Zargin Dala Miliyan 9.7 na tallafa wa ta’addanci: EFCC ta shigar da sabuwar ƙara kan kwamishinan kuɗi na Bauchi da wasu mutane
A cikin tuhuma ta farko, an zargi Adamu da hadin baki da wasu mutane biyu wajen aikata laifin tsakanin watan Yuni da Disamba na shekarar 2023, lokacin da yake aiki a matsayin manajan reshen Polaris Bank a Bauchi.
Zargin ya nuna cewa sun taimaka wajen sauyawa, boyewa da amfani da kudade kimanin N4,650,000,000 da aka bayar a matsayin rancen banki domin samar da babura, alhali ba a aiwatar da hakan ba.
Kotu ta kuma ji cewa sauran tuhume-tuhumen sun shafi rikewa da kuma yada kudaden da ake zargin sun fito daga aikata laifi, inda aka ce an wuce da wani bangare na kudaden ta hannun asusun wasu mutane da kamfanoni.
Haka kuma wasu daga cikin kudaden sun shiga asusun Ayab Agro Products and Freight Company Ltd.
Bayan karanta tuhumar, wadanda ake tuhuma sun musanta dukkan tuhume-tuhumen, daga nan ne lauyan Adamu ya roki kotu ta ba shi beli, yana mai bayyana cewa bukatar beli ta riga ta kasance a gaban kotu, tare da rokon a ba shi beli cikin sassauci.
Lauyan EFCC ya bukaci kotu ta ki amincewa da belin, yana mai nuna cewa an shigar da takardar adawa da bukatar beli, tare da neman a gaggauta sauraron shari’ar. Alkalin kotun ya bayyana cewa za a bayar da ranar yanke hukunci kan belin cikin gaggawa.
A karshe, kotun ta bayar da umarnin tsare Yakubu Adamu a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan bukatar belin, tare da dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa kotun ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar kara gurfanar da wasu mutane a cikin shari’ar.













































