Gobara ta kone wani babban kamfani siyar da kayan daki mai suna Alibert Furniture ma kan hanyar Murtala Mohammed a cikin birnin Kano.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa gobarar da ta tashi da sanyin safiyar ranar Litinin, ta lalata gaba daya sassan kamfanin dake kallon Kano Club, wanda ke makwabtaka da kamfanin Fridabs mamallakin jaridar Solacebase, inda barnar da gobarar tayi ya shafi ofishin jaridar Solacebase.
Tuni aka garzaya da masu gadin kamfanin su 2 da suka samu raunuka asibiti a yayin tashin gobarar.
Zuwa yanzu ba’a tabbatar da musabbabin gobarar ba, amma shaidun sun danganta lamarin da tartsatsin wutar lantarki daga na’urar taranfoma na kamfanin.
Ko da yake jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar, har yanzu wutar na ci gaba da ruruwa a wasu sassa na kamfanin.
HOTUNAN GOBARAR













































