‘Yan bindiga sun kashe sama da mutane 20 tare da lalata dukiyoyi na miliyoyin Naira a karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna a jiya Asabar.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
Aruwan ya bayyana cewa sojoji da ‘yan sanda sun kai wa gwamnati rahoton cewa an kashe mutane sama da 20 a hare-haren ‘yan bindiga a kauyukan karamar hukumar.
Ya ce Yan bindiga sun kai hari kauyukan Kauran Fawa, Marke da Riheya da ke Idasu, karamar hukumar Giwa, inda suka kashe mutane sama da 20.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufai wanda ya samu rahoton cikin alhini, ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa.
Ya kara da cewa Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar da abin ya shafa, ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna da ta gudanar da tantancewar cikin gaggawa a yankin domin bayar da agaji.
Samuel Aruwan ya ce Za a buga sunayen wadanda aka kashe da zarar an tabbatar da karin bayani daga gwamnatin jihar Kaduna.













































