Rahotanni na bayyana cewa an illata jagoran ƴan ta’adda masu fashin daji, Bello Turji bayan da ya samu muggan raunuka yayin da jiragen yaƙin sojoji su ka kai hari maɓoyarsa da kuma sansanonin ƴan tashin daji dake Sakoto da Zamfara.
Haka-zalika jiragen yaƙin gamayyar rundunar dakaru ta Sintirin Haɗin Kai sun hallaka yan bindiga a dajikan Zamfara da Sakkwato da sassafiyar Lahadi.
Rahotanni sun bayyana cewa dajikan da aka kai hari sun hada da Shinkafi da ke Zamfara, Bafarawa, Isa da kuma Sabon Birni a Sakkwato.
Kawo yanzu dai ba a tantance adadin yan ta’addan da a ka hallaka a hare-haren ba.












































