Kano: Ƴan sanda sun gurfanar da mutane 29 da ake zargi da kashe DPO

Police badge (2)

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wasu mutane 29 da ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa Baturen ‘yan sanda na garin Rano, CSP Baba Ali, wanda aka kashe a wani rikici da ya barke a karamar hukumar ta Rano.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a yau Alhamis, ta ce an gurfanar da wadanda ake zargin ne a gaban kotun majistare mai lamba 20 da ke Noman’sland bayan gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Sanarwar ta ce mutane 14 daga cikin wadanda ake zargin an tuhume su da laifin kisan kai da kuma laifukan da suka shafi hada baki wajen tada zaune tsaye, da kumac aikata laifukan haddasa munanan raunuka, da kuma sata.

Wadanda ake tuhuma kan kisan DPO din sun hada da Bala Yusuf da Bala Mohammed da Abdulrashid Ibrahim sai Abdullahi Salisu Kere da Sadiq Buhari da Yunusa Adamu da Musa Minkaila, sai Mamuda Mohammed da Ismail Mamuda da Usman Shu’aibu da Musa Hassan Black da Abdulrashid Munkail da Umar Ado Nadada da kuma Sabitu Abubakar.

Sanarwar ta kuma ce, dukkanin mutane 14 din mazauna karamar hukumar Rano ne, Baya ga manyan wadanda ake zargin, an tuhumi wasu 15 da laifukan da suka shafi tashe-tashen hankula da hada baki wajen tada hankalin jama’a da kuma barna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here