San takarar Mataimakin gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata na shekarar 2023, Murtala Sule Garo, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi addu’o’in samun zaman lafiya da hadin kai da kuma ci gaba a Nijeriya, yayin gudanar da bukukuwan babbar Sallah ta bana.
Alhaji Murtala Sule Garo, ya buƙaci hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu tare da raba ta ga manema labarai a daren yau Alhamis, a wani ɓangare na saƙonsa na barka da Sallah.
Garo ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan ’yan wasan Kano 22 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kwanan baya a lokacin da suke dawowa daga gasar wasanni ta kasa da aka gudanar a jihar Ogun.
Ya kuma bukaci jama’a da su rika tunawa da su da iyalansu a cikin addu’o’insu musamman ma a wannan lokaci na ibada.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ina mika sakon gaisuwata ga al’ummar Musulmin jihar Kano da ma fadin Nijeriya baki daya, da fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya, Allah ya kuma kara dankon zumunci a tsakaninmu.
“Ina kuma yin addu’ar Allah ya jikan ‘yan uwanmu da suka rasu a hatsarin kwanan nan, Allah ya gafarta musu ya kuma bai wa iyalansu haƙuri,” in ji Garo.
Ya kuma kara jan hankalin mawadata da su rika taimakon marasa galihu tare da inganta zaman lafiya a cikin al’ummarsu a wannan lokacin na bukukuwa.













































