Archbishop Desmond Tutu ya rasu yana da shekara 90

Desmond Tutu
Desmond Tutu

Archbishop Desmond Tutu, ɗan Afirka ta Kudu wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel, ya rasu yana da shekara 90.

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da rasuwar tasa cikin wata sanarwa.

“Mun sake shiga wani yanayin alhini na rabuwa da zamanin manyan ‘yan Afirka ta Kudu waɗanda suka samar mana ‘yanci,” a cewarsa.

  • Shugaba Ramaphosa ya ce Tutu “shugaban addini ne mai kwarjini, mai yaƙi da gwamnatin wariya kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙi na duniya”.

Mista Tutu na cikin ‘yan ƙasar da aka fi sani a gida da wajenta. Ya taimaka ƙwarai wajen kawo ƙarshen mulkin wariya.

Yana cikin na gaba-gaba da suka yaƙi gwamnatin wariyar launin fata, kamar Nelson Mandela, wadda Turawa suka gudanar a Afirka ta Kudu daga 1948 har zuwa 1991.

An ba shi kyautar zaman lafiya ta Nobel a 1984 saboda rawar da ya taka wajen korar gwamnatin wariyar.

Mutuwar shahararren malamin addinin Kiristan ta zo ne ‘yan makonni da rasuwar shugaba na ƙarshe a gwamnatin wariya, FW de Clerk, wanda ya mutu yana da shekara 85.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here