A yau Laraba, 30 ga watan Nuwamba ne aka sa ran za a gurfanar da dalibin Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Aminu Adamu Mohammed wanda ya caccaki uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, BBC Hausa ta rahoto.
An dai yi zargin cewa jami’an tsaro sun kama matashi Aminu tare da tsare shi tsawon kwanaki 13 ba tare da gurfanar da shi don ya fuskaci shari’a ba.
A yanzu haka dai babu tabbaci kan tuhume-tuhumen da hukumomi za su yi wa matashin wanda jami’ai suka dauke ba tare da sanin hukumomin makarantarsa ba bisa umurnin Aisha Buhari.
Batun gurfanar da Aminu na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa da wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam da wasu manyan masu fada aji ke kiraye-kiraye tare da neman a sake shi.













































