Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta bukaci hukumar ‘yan sanda da ta binciki wasu ‘ya’yan jam’iyyar NNPP a jihar da a yanzu ake tsare da su, bisa zargin kai hari tare da lalata kadarorin yakin neman zaben jam’iyyar APC a karamar hukumar Gwale.
Idan za a iya tunawa Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a ranar Litinin din da ta gabata ne dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar bijirewa sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya sakamakon hare-haren da wasu ‘yan daba na APC suka kai wa mambobinsa.
Jam’iyyar APC cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Gawuna/Garo kuma kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar, ta ce ‘yan daban sun haifar da rudani matuka tsakanin al’umma.
Sanarwar ta ce harin ya biyo bayan tattaki da dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya yi bayan halartar bikin daurin aure a yankin.
Sanarwar ta ce, abin takaici ne yadda bayan faruwar lamarin Yusuf ya dora laifin a kan jam’iyyar APC, har ma ya yi kira da a kama shugabanta, Alhaji Abdullahi Abbas.
A cewar sanarwar, Garba ya zargi jam’iyyar NNPP da yin farfaganda da karyar gangan domin haifar da hargitsi gabanin babban zabe.
Kwamishinan ya kuma yi Allah-wadai da kalaman da shugaban NNPP, Haruna Umar Doguwa ya yi na kalaman nuna kiyayya da ke iya haddasa tashin hankali sakamakon aukuwar lamarin a karshen mako.













































