Mawallafin jaridar Nigerian Tracker ya zama ma’ajin kungiyar kafafen yada labaran Internet na Arewa

WhatsApp Image 2025 02 03 at 06.44.04 612x430

Kungiyar ‘yan jarida ta Arewa Online Media Reporters and Publishers (NORP) ta zabi sabbin mambobinta na kwamitin zartaswa na kasa.

Zaben an gudanar a Kaduna karkashin kwamitin zaben na kungiyar.

Kwamared Musa Mohammed daga jihar Kaduna shi ne ya zama sabon shugaban zartaswa na kasa a zabe inda ya samu kuri’u 287 tare da kayar da abokin takararsa, Comrade Lynn Adda, tsohon shugaban NUJ na jihar Taraba, wanda ya samu kuri’u 138.

Kwamared Femi Adi daga jihar Kogi ya zama babban sakataren jam’iyyar na kasa da kuri’u 210 bayan da ya doke Comrade Rayyan Al-Hassan wanda ya samu kuri’u 207.

A tsarin mulkin kungiyar, a kan mika kujerar mataimakin sakatare na kasa da Mataimakin shugaba na kasa ga mutanen da suka zo na biyu, don haka, Comrade Lynn Adda da Comrade Rayyan Al-Hassan suka zama mataimakin shugaba na kasa kuma mataimakin sakataren kasa.

Sauran wadanda suka fito babu hamayya sun hada da Comrade Zaharaddeen Ishaq Zailani – Sakataren kudi na kasa, Comrade Ibrahim Suleman mataimakin sakataren kudi na kasa, da kuma Comrade Abbas Yusha’u Yusuf Ma’ajin kudi na kasa.

A jawabinsa na karramawar, Kwamared Musa Mohammed ya bukaci ‘ya’yan kungiyar da ke fadin jihohin Arewa 19 da su yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaki da labaran karya da kuma inganta shugabanci na gari.

A cewarsa, shafukan sada zumunta za su kasance abin dogaro ne kawai don yada bayanai idan kwararrun ‘yan jarida suka karbe su da kuma amfani da su ta hanyar kwarewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here