Jami’an tsaro sun harbe mutane hudu tare da raunata wasu 16 a wani atisayen ruguje gidaje da gwamnatin jihar Kano ta gudanar a Rimin Zakara da ke kusa da jami’ar Bayero ta Kano a karamar hukumar Ungogo.
SolaceBase ta rahoto cewa rusau din, wanda ya shafi gine-gine sama da 18, ya faru ne a daren Lahadi.
A cewar mazauna yankin, atisayen ya fuskanci turjiya saboda rashin sanarwar da aka riga aka yi musu.
Wani ganau mai suna Mallam Sunusi Dan-Baba, ya shaidawa SolaceBase cewa tawagar rusau sun iso da daddare, inda suka fara ruguza gidaje da shaguna.
Ya bayyana cewa an shafe sama da shekaru 20 ana takaddamar filin tsakanin Jami’ar Bayero Kano da mazauna yankin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Kano, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa an tura jami’an tsaro da suka hada da NSCDC yankin domin kare kadarorin gwamnati kuma sun fuskanci turjiya daga mazauna yankin.
“Mun je can ne domin samar da tsaro da kuma kare kadarorin gwamnati. Sai dai mazauna yankin sun far wa jami’an mu, inda suka raunata daya daga cikin jami’an mu, sannan suka lalata mana motocin mu,” inji Abdullahi.
Lamarin dai ya janyo cece-ku-ce a tsakanin mazauna yankin, inda suke neman a gudanar da bincike kan kisan mutanen da aka yi da kuma yin karin haske dangane da mallakar filin da ake takaddama a kai.
Duk kokarin jin ta bakin daraktan hulda da jama’a na Jami’ar Bayero Kano Malam Lamara Garba bai yi nasara ba domin wayarsa a kashe take.