Sojin Najeriya sun bayyana dalilin sakin ‘yan ta’addan gwamnatin Borno

Sojin, Najeriya, 'yan ta'adda, jihar, borno, gwamnatin, sakin, dalilin
Hedikwatar tsaro ta ce ta saki mutane 313 da ake zargi da ta'addanci ga gwamnatin Borno bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri...

Hedikwatar tsaro ta ce ta saki mutane 313 da ake zargi da ta’addanci ga gwamnatin Borno bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri.

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja, ya ce an tsare wadanda ake zargin ne bisa tuhuma, amma ba’a samu wata shaida a kansu ba a karshen binciken.

A cewarsa, ma’aikatar shari’a ta tarayya ce ta shigar da kararrakin, inda kotun ta bayar da umarnin a sake su.

Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya na shirin kwato jirage 2 na NCAT Zariya da aka sayar

“A bisa ga haka an mika su ga gwamnatin jihar Borno domin ci gaba da daukar mataki,” inji shi.

A halin da ake ciki, dakarun Operation Hadin Kai sun samu gagarumar nasara a kan ‘yan ta’addar Boko Haram da ISWAP, inda suka kashe mutane da dama tare da kame abokan aikinsu a cikin wannan mako.

Buba ya ce kwamandojin ‘yan ta’adda da mayakan sun kuma mika wuya ga sojoji a kananan hukumomin Jere da Chibok da Monguno da Gwoza da Bama a Borno, da kuma karamar hukumar Madagali ta Adamawa.

Karin labari: Rundunar sojin Najeriya  na neman mutane 8 ruwa a jallo da take  zargi suna da hannu wajan kisan  sojoji a Delta

A cewarsa, rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ta gudanar da wasu hare-hare ta sama kan ‘yan ta’adda a Arina Woje da Tumbum Shitu kusa da tafkin Chadi a ranakun 22 ga watan Maris da 24 ga watan Maris.

“An lura da wuraren suna aiki tare da ayyukan ‘yan ta’adda da kayan aiki.

“Saboda haka, an samu wurin da aka kai hari da rokoki da bama-bamai, kuma binciken da aka yi a yakin ya nuna cewa an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata musu kayan aikinsu.

Karin labari: “Zamfara a yanzu ita ce babbar wajen ta’addanci” – Gwamna Lawal

“Baki daya, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 52, sun kama 137 tare da kubutar da mutane 78 da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas a cikin makon da ake nazari.

“Sojoji sun kwato bindigogin M56 guda uku da AK47 guda 40 da kuma bindigogin PKT guda uku da bindigogi 13 da gurneti guda biyu sai bama-bamai guda 889 na ammo na musamman 7.62mm da kuma 310 na 7.62mm NATO”  da sauran makamai in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here