
Daga: Khadijah Waziri da Ummulkhairi Abubakar
Rundunar sojojin Najeriya ta ayyana mutane takwas da take nema ruwa ajallo, wanda take zarginsu da kisan sojin Najeriya guda sha bakwai a yankin okuama dake jihar delta.
A cikin mutanen da take nema sun hada da maza takwas da kuma mace daya.
Mutanen da take nema sun hada da Akevwru Daniel Omotegbono (Amagbem); Prof. Ekpokpo Arthur; Andaowei Denis Bakriri; Igoli Ebi; Akata Malawa David; Sinclair Okili; Clement Ikolo Oghenerukvwe da kuma Reuben Baru.
Daraktan rundunar mai kula da kafofin yada labarai Maj.-Gen. Edward Buba neya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai ranar alhamis a Abuja.
Buba ya kara da cewa rundunar sojojin baza ta kara barin irin wannan kisan na sojojin ya kara faruwa ba.
Ya kuma yi kira ga alumma da su bawa rundunar sojin hada kai da sauran jamian tsaro na kasar nan wajen bada bayanan sirri da zasu taimakawa rundunar wajen kama wadanda take zargi.












































