An samu baki biyu tsakanin ‘yan sanda da NSCDC kan harin da aka kai wa ayarin motocin Aregbesola a Osun

4125A066 0AB8 48F6 A3A8 FBACE42D8ED2
4125A066 0AB8 48F6 A3A8 FBACE42D8ED2

Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta ce jami’an tsaro a cikin ayarin motocin ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne suka kai harin da ya faru a Old Garage dake Osogbo ranar Litinin.

A yayin da al’amarin ya faru, an ji karar harbe-harbe, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin jama’ar yankin, yayin da ayarin motocin suka bi ta Old Garage zuwa Unguwar Oke Fia a Osogbo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce jami’an tsaron farin kaya da na Civil Defence, da na hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya da ke cikin ayarin motocin Aregbesola, sun yi harbi a lokacin da suke wucewa ta Old  Garage da MDS a Osogbo babban birnin jihar.

A cikin sanarwar, Opalola, wanda kuma ya ce harbin ya haifar da firgici, ya ce an gano harsasai 13 bayan ayarin motocin sun bar yankin.

Sai dai Wata sanarwa da Olabisi Atanda, mai magana da yawun NSCDC a Osun ya fitar ta ce, “wasu ‘yan bindiga ne da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kan ayarin motocin tsohon gwamnan jihar Osun kuma minista, ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranar litinin da misalin karfe 18:40 a kusa da unguwar Old Garage a Osogbo Babban Birnin Jihar.

“Jami’an tsaro na Ministan sun yi nasarar tarwatsa barayin tare da kawo zaman lafiya a yankin.

“Kwamandan Emmanuel Ocheja ya ce jihar Osun jiha ce mai zaman lafiya kuma rundunar za ta ci gaba da samar da kyakkyawan tsarin tsaro na kowa da kowa a jihar, kamar yadda doka ta tanada da ayyukan rundunar Ƙwarewa da rashin son kai kalma ce ta NSCDC a kowane lokaci.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here