Hukumar shirya jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WAEC) ta ce za a ba wa daliban da zasu rubuta jarabawar wadanda ba su da lambar shaida zama dan kasa (NIN) damar rubuta jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) ta bana.
Shugaban ofishin WAEC na kasa (HNO), Mista Patrick Areghan, ya ba da wannan tabbacin a wani taron manema labarai don sanar da fitar da sakamakon WASSCE ta 2021 bangaren dalibai masu zaman kansu ranar Litinin a Legas.
Areghan ya yi magana ne a kan yadda wasu iyayen suka firgita, bayan da ma’ajiyar bayanai ta NIMC ta samu matsala a kwanakin baya.
Ya bayyana cewa ya zama ruwan dare a samu irin wadannan kalubale a wasu lokuta tare da bullo da sabbin tsare-tsare, yana mai cewa komai zai daidai a cikin lokaci.
“Lokacin da NIMC ta fuskanci kalubale, mutane da yawa sun firgita, musamman ganin yadda dalibai suke tururuwar yin rajistar WASSCE na 2022 na makarantu.
“Na tuna a fili cewa kafin yanzu, mun sanar da cewa dalibai ba za su iya rubuta WASSCE ba sai da NIN, wato babu NIN, babu jarrabawa.
“Muna so mu bayyana a nan cewa sakamakon kalubalen baya-bayan nan da hukumar NIMC ta yi, dalibai suna da ‘yancin rubuta jarabawar ba tare da gabatar da NIN ba.
“Wadanda ke da katin NIN za su iya zuwa tare da shi zuwa makaranta, amma wanda basu da shi zasu yi jarabawa ba tare da wata matsala ba.
“Kowane yaro dan Najeriya zai rubuta jarabawar. Rashin mallakar NIN ba zai hana kowane yaro rubuta jarrabawar ba. Bai kamata ya zama cikas ba saboda mun umurci shugabannin makarantu su tura jerin sunayen daliban da basu da NIN.
Da yake sanar da sakamakon jarabawar WASSCE na dalibai masu zaman kansu na shekarar 2021, Shugaban ya ce adadin ‘yan takara 52,973 ne suka yi rajista, inda 51,444 daga cikinsu suka rubuta jarabawar.
Ya yi nuni da cewa, daga cikin adadin wadanda suka zana jarrabawar, 49,584 ke wakiltar 96. Kashi 38 cikin 100 na su an kammala tantance su da kuma fitar da su, yayin da wasu 1,860, wanda ke wakiltar kashi 3.62 cikin 100, har yanzu ana ci gaba da tantancewa.
A cewarsa, hakan ya faruwa ne sakamakon wasu kura-kurai dalibai suka samu, yana mai cewa, ana kokarin gaggauta kammala aikin domin baiwa dukkan wadanda abin ya shafa damar tantance sakamakonsu gaba daya, sannan a fitar da su daga baya.










































