Majalisar wakilan Najeriya na shirin kwato jirage 2 na NCAT Zariya da aka sayar

Majalisar, wakilan, Najeriya, kwato, jirage, NCAT, Zariya, sayar
Majalisar wakilan Najeriya ta sha alwashin kwato jirage 2 na Bell 206L4 BZB da Bell M2061- L4 na kwalejin fasahar jiragen sama ta Najeriya NCAT Zariya da aka...

Majalisar wakilan Najeriya ta sha alwashin kwato jirage 2 na Bell 206L4 BZB da Bell M2061- L4 na kwalejin fasahar jiragen sama ta Najeriya NCAT Zariya da aka sayarwa wasu mutane masu zaman kansu.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da kadarorin jama’a, Sanata Ademorin Kuye ne ya bayyana haka a zaman binciken da aka yi kan sayar da jiragen guda biyu da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Kuye ya nuna damuwarsa kan yadda aka sayar da jirage masu saukar ungulu guda biyu ga wasu mutane masu zaman kansu a lokacin da kwalejin ta kasance ba ta da jirgi mai saukar ungulu da za’a yi atisaye.

Karin labari: Gwamnan Kano ya tallafawa Alhazai 2,906 kowannen su da Naira 500,000

Kwamitin ya kuma nuna shakku kan yadda ake siyar da jirage masu saukar ungulu saboda hukumomin tsaro da suka hada da sojojin saman Najeriya da na ruwa da kuma ‘yan sanda sun nuna sha’awar siyan su.

Sai dai hukumar ta NCAT ta musanta zargin hukumomin tsaro.

Hukumomin tsaro uku, a cewar bayanai daban-daban, ba wai kawai sun nuna sha’awar siyan jirage masu saukar ungulu ta hanyar rubutawa ba, har ma sun ziyarci kwalejin amma an hana su sayen su.

Karin labari: BDC sun karyata sayar da Dala daga 900 zuwa Naira 1,000

Mista Shaka Imalighwe, Mukaddashin Rector, NCAT, ya ce duk da cewa shi ne mataimakin shugaban kwalejin a lokacin da ake sayar da jirage masu saukar ungulu, ba ya cikin tawagar kwamitin da suka taimaka wajen siyar da kayayyaki.

Imalighwe ya ce ya karbi ragamar kula da kwalejin ne a matsayin riko a watan Janairun 2024.

Kwamitin ya ce duk da rokon da NCAT ta fara yi na samar da wasu takardu dangane da tsarin da ya kai ga siyar da jirage masu saukar ungulu a watan Mayun 2023, amma ba su samu ba.

Karin labari: “Tinubu ya san manyan Najeriya da ke hada kai da ‘yan bindiga” – Matthew Kukah

Wannan, a cewarsa, ya kasance dangane da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya FEC, da ma’aikatar sufurin jiragen sama da kuma buga jaridun da ke tallata aniyar sayar da jirage masu saukar ungulu.

Imalighwe ya shaida wa kwamitin cewa jirage masu saukar ungulu suna aiki kuma hukumomin da abin ya shafa suna kula da su lokacin da aka sayar da su.

Mukaddashin shugaban kwalejin ya kuma tabbatar wa da ‘yan majalisar cewa a halin yanzu babu wani jirgi mai saukar ungulu a cibiyar da za’a horas da su.

Karin labari: Shugaba Tinubu ya sake sabon nadi

‘Yan majalisar dai sun yi zargin cewa ba daidai ba ne NCAT ta yi amfani da wani mai gwanjo mara izini wajen siyar da jirage masu saukar ungulu.

Kwamitin ya umarci tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma na yanzu da ya bayyana a gaban sa a zaman bincike na gaba.

Haka kuma an gayyaci ma’aikatar ayyuka da ma’aikatar kudi ta MOFI da shugabannin kwalejin na baya da na yanzu da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here