Tinubu ya sake sabon nadi

PSC, FCCPC, Shugaba, Tinubu, aike, sunayen, mutane, Majalisar, Dattawa
Shugaba Tinubu ya mika sunayen mutane uku da aka nada domin tantancewa da tabbatar da nadinsu a matsayin shugaba da sakatare da kuma memba na Hukumar...

Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Manjo-Janar Adamu Garba Laka a matsayin sabon kodinetan cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa a ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Talata.

Karin labari: Gobara ta lalata motoci 8 da rumfuna a jihar Kano

Ta ce Janar Laka ya yi ayyuka daban-daban a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda ya yi amfani da dabarun da ya dace don kaskantar da kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Ya kuma yi aiki a Saliyo da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango a karkashin Majalisar Dinkin Duniya kuma yana cikin tawagar Najeriya a atisayen AFRICOM na Amurka a Senegal.

Karin labari: Majalisar Togo ta amince da kundin tsarin mulkin kasar da ta yiwa kwaskwarima

“Ya yi digirin-digirgir a fannin tsaro na kasa daga jami’ar tsaro ta kasa Pakistan, da kuma fannin nazarin harkokin kasa da kasa da dabarun yaki, makarantar horas da tsaro ta Najeriya.

“Shugaban kasa yana tsammanin cewa Janar Laka zai kawo kwarewarsa a cikin wannan muhimmiyar rawar don kawar da barazanar tsaro yadda ya kamata ta hanyar riga-kafi, mai himma, da kwazon yaki da ta’addanci,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here