Majalisar Togo ta amince da kundin tsarin mulkin kasar da ta yiwa kwaskwarima

Shugaban, kasar, Togo, Faure Gnassingbé, majalisar, amince, kundin, tsarin
‘Yan majalisar Togo sun amine da kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya sauya tsarin mulkin kasar daga na shugaban kasa mai cikakken...

‘Yan majalisar Togo sun amine da kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya sauya tsarin mulkin kasar daga na shugaban kasa mai cikakken iko zuwa na Faraminista.

Sabon daftarin dokar dai ya nuna cewa, ‘yan majalisa ne za su rinka zabar shugaban kasa na tsawon wa’adi guda, ba jama’ar kasar ba, kamar yadda aka saba a baya.

Karin labari: Kotu Ta Yankewa Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Wannan sauyin dai na zuwa ne kasa da wata guda da za’a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a kasar ta Togo, sai dai ba’a san lokacin da za’a fara amfani da sabon kundin tsarin mulkin ba da ‘yan majalisu 89 suka amince da shi, daya kuma ya hau kujerar naki sannan ragowar dayan ya kauracewa kada kuri’ar amincewa.

‘Yan majalisar da suka fito daga jam’iyar da ke mulkin kasar ta UNIR ne suka gabatar da kudirin sauya fasalin kundin tsarin mulkin kasar da kuma amincewa da shi.

Karin labari: Majalisar dokokin Kano ta rushe shugabannin hukumar daukar ma’aikata

Jam’iyyar adawar kasar da ta kauracewa shiga zaben ‘yan majalisar kasar da aka gudanar a shekarar 2018 saboda dalilan sabawa ka’ida, ba tada wakilci a majalisar kasar.

Kundin tsari mulkin da kasar ke amfani da shi yanzu haka an kirkire shi ne tun 1992, to amma an yi masa gyare-gyare sau da dama, kuma na karshe shi ne wanda aka yi a 1999, a karkashinsa, ana zaben shugaban kasa wa’adin shekaru 5 ne tare da damar sake tsayawa karo na biyu kawai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here