Yanzu -yanzu: Gwamna Douye Diri ya fice daga jam’iyyar PDP

Douye Diri 720x430

Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Diri ya bayyana wannan mataki nasa ne a ranar Laraba a dakin taron majalisar zartarwa da ke fadar gwamnatin jihar Bayelsa, inda bai bayyana wace jam’iyya zai koma ba.

Rahotanni sun nuna cewa mambobi 23 na majalisar dokokin jihar, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, sun mara masa baya a wannan mataki.

Ficewar gwamnan ta faru ne bayan awa 24 da takwaransa na jihar Enugu, Peter Mbah, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Matakin na gwamna Diri ya janyo cece-kuce a tsakanin jama’a, musamman ganin cewa yana daya daga cikin gwamnonin da aka san suna tare da jam’iyyar PDP tun da farko.

Ana sa ran gwamnan zai bayyana sabuwar jam’iyyar da zai shiga nan gaba kadan yayin da siyasar jihar Bayelsa ke ɗaukar sabon salo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here