Jami’ai a yammacin Afghanistan sun ce mutane 18 ciki har da wani fitaccen malami sun mutu a wani hari da aka kai wani masallaci a birnin Herat.
Mai magana da yawun Taliban, ya ce za a hukunta duk wadanda aka samu da laifin kisan Mawlawi Mujib Rahman Ansari.
Ansari shi ne malamin addinin Musulunci na hudu da ke da kusanci da Taliban da aka kashe a kasa da watanni biyu.
Wasu daga cikin hare haren da aka kai IS ta ce ita ta kai su.
Harin ya faru ne a yayin da ake sallar Jumma’a a masallacin Guzargah.
Akwai wasu mutanen fiye da 20 da suka samu raunuka a cikin fashewar abin da aka kai masallacin sannan kuma asibitocin da ke birnin na ta kai kawo wajen yi wa mutanen da abin ya shafa magani.
Har yanzu ba a kai ga gano wadanda suka kai harin ba, to amma ‘yan kungiyar IS sun fitar da wani bidiyo in da suke yi wa malamin barazana.













































