Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta ƙasar Laberiya (NPA) ta kori wasu manyan jami’ai 10 bayan an zarge su da cin hanci da rashawa.
Sekou Hussein Dukuly, Manajan Darakta na NPA, ya ce mutanen suna da hannu cikin almundahana.
Ya ce an samu mutanen da laifi bayan bincike na cikin gida.
Karin labari: Gwamnan Kano ya karbi bakuncin tawagar bankin Duniya
Mista Dukuly ya ce an aika da karar zuwa ga ‘yan sanda domin gurfanar da su gaban kuliya.
Sai dai wasu daga cikin waɗanda ake zargin suna shirin daukar matakin shari’a a kan hukumar ta NPA.
“Na samu wasikar kora daga hukumar ne kawai, amma lauyoyina sun ce kada in yi tsokaci kan zarge-zargen,” Pewu Flomoku, daya daga cikin wadanda ake tuhumar.
Karin labari: Gwamnatin Tinubu ta musanta coge a kasafin kuɗin ƙasar
Tsohon manajan tashar jiragen ruwa na Buchannan, Civicus Barsi-Giah ya kira matakin a matsayin siyasa kuma ya ce bai sami takardar dakatarwa a hukumance ba kuma ya ce ba a sanar da shi wani bincike na cikin gida ba.
Hukumar ta NPA ta kuma bayar da rahoton wasu jami’an tashar ruwa guda bakwai bisa zargin haɗa baki wajen sace manyan motoci 20 na shinkafa a tashar, a makon jiya.
Matakin na NPA ya zo daidai da sanarwar da shugaban ƙasar Joseph Boakai ya bayar inda ya ce yana kafa wata rundunar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar.