
Fadar shugaban Najeriya ta musanta zargin yin coge a kasafin kudin 2024 wanda Shugaban kasar ya sanyawa hannu a watan Janairu.
Ɓangaren zartarwar ta mayar da martani ne a wata hira da BBC, wanda shugaban ƙungiyar majalisar dattawan ƙasar na yankin arewa, Sanata Abdul Ningi ya yi zargin cewa kasafin kuɗin da bangaren zartarwa ke aiki da shi ba shi ne majalisun dokokin kasar suka rattabawa hannu ba.
Karin labari: Al-Qa’ida ta sanar da mutuwar shugabanta a Yemen
Sai dai mataimaki na musamman ga shugaban kan yada labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya ce ba kamshin gaskiya a zargin.












































