Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta aiwatar da ayyuka sama da 1,508 na ci gaba da suka kai darajar Naira biliyan 928 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kwamishinan Ma’aikatar kula da Kwangiloli da Sanya ido kan Ayyukan Gwamnati, Kwamred Nura Ma’aji Sumaila ne ya bayyana hakan a wani taro da manema labarai na kasa da kasa a ranar Asabar, inda ya jero nasarorin gwamnatin a fannin ci gaban ababen more rayuwa, ayyukan jin dadin jama’a da kuma inganta hidimar gwamnati.
A cewar kwamishinan, an kammala ayyuka 799, yayin da 709 ke kan matakai daban-daban na kammalawa.
Ya kara da cewa wannan adadin bai hada da ayyukan mazabu 619 da ake aiwatarwa a halin yanzu a kananan hukumomi 44 ta hanyar ‘yan majalisar dokokin Jihar Kano.
Sumaila ya ce gwamnatin ta ci gaba da jajircewa wajen sabunta ababen more rayuwa da tabbatar da ci gaba daidai gwargwado a birane da kauyuka, yana mai bayyana cewa an gudanar da ayyukan ne bisa ka’idojin gaskiya, samin darajar kudi da ingantacciyar aiwatarwa.
“Gwamnatin Jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta ci gaba da nuna jajircewa wajen sabunta ababen more rayuwa, ci gaban jin dadin jama’a da inganta hidimar da ake yi wa jama’a a fadin jihar,” in ji shi.
Ya bayyana cewa ayyukan sun shafi sassa daban-daban da suka dace domin inganta rayuwar ‘yan kasa da kuma karfafa ginshikin tattalin arzikin jihar.
Da ya ke bayar da cikakken bayani kan ayyukan, kwamishinan ya ce ayyukan sabunta birane sun kai kwangiloli masu darajar sama da Naira Biliyan 169, wadanda suka hada da gyaran hanyoyi, gina magudanan ruwa da sauran gyare-gyaren birni.
Ya kara da cewa gwamnatin ta bai wa kamfanoni kwangilolin gina hanyoyin kilomita biyar a kananan hukumomi 38 masu darajar sama da Naira Biliyan 118, a matsayin wani kokari na inganta hada-hada da saukaka zirga-zirga a fadin jihar.
A fannin tsaro, Sumaila ya ce gwamnatin ta sanya sama da Naira Biliyan 6.863 wajen gina ofisoshin ‘Yan Banga a Jihar Kano a kananan hukumomi 36 domin karfafa tsaro a cikin al’umma da inganta tsaron jama’a.
Ya kuma bayyana cewa ana aiwatar da ayyukan more rayuwaa kauyuka masu darajar sama da Naira Biliyan 397 a kananan hukumomi 44, wadanda suka shafi ilimi, lafiya, hanyoyi da sauran shirye-shiryen jin dadin jama’a da aka tsara don inganta rayuwa a kauyuka.













































