Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya zargi ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da haddasa tuhumar daukar nauyin ta’addanci da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar kan kwamishinan kudi na jiharsa, Yakubu Adamu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a tashar talabijin ta Channels a ranar Alhamis, inda ya yi ikirarin cewa Wike na amfani da tasirinsa wajen karkatar da hukumomi, bayar da cin hanci, sayar da filaye da kuma amfani da dukiyarsa domin cimma muradun siyasa.
Ya ce yana da tabbacin cewa akwai hannun wasu mutane a bayan lamarin, yana mai alakanta hakan kai tsaye da ministan Babban Birnin Tarayya, wanda ya bayyana a matsayin wanda ke iko da wasu manyan hukumomi da kuma amfani da su wajen kai hari a kansa da gwamnatinsa.
Bala Mohammed ya kuma zargi tsohon babban akantansa da yin aiki tare da Wike, yana mai cewa mutumin na taka rawa a matsayin shaida a shari’ar da hukumar EFCC ke yi wa kwamishinan kudinsa da ke fuskantar tuhuma.
Karin labari: Shugaban majalisar Dattawa Akpabio ya janye duk wata ƙarar ɓata suna bayan shawarwarin limami
Gwamnan ya kara bayyana Wike a matsayin barazana ga siyasar kasa, yana mai cewa ministan na jawo cikas ga tafiyar gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, tare da raunana jam’iyyar PDP daga ciki.
Ya tunatar da cewa a baya ya riga ya zargi gwamnatn tarayya da amfani da hukumar EFCC wajen tsangwamar shi da jami’an gwamnatinsa, saboda kin amincewarsa da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Hukumar EFCC ta shigar da kara a baya kan kwamishinan kudi na jihar Bauchi, Yakubu Adamu, tare da wasu jami’an gwamnatin jihar, kan zargin daukar nauyin ta’addanci da ya kai dalar Amurka miliyan 9.7.












































