Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya umurci lauyoyinsa da su janye dukkan ƙarar bata suna da ke gaban kotu, bayan ya ce shawarwarin da wani limami ya bayar a yayin taron ibadar sabuwar shekara sun yi tasiri a kansa.
Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa daga ofishin yada labarai na shugaban majalisar dattawa da ke Abuja, inda aka bayyana cewa matakin ya biyo bayan tunani mai zurfi da Akpabio ya yi kan muhimmancin zaman lafiya da yafiya.
A yayin da yake jawabi a ranar Alhamis a cocin Sacred Heart Parish da ke Uyo, Akpabio ya bayyana cewa ya shigar da kusan ƙara tara a gaban kotu kan mutanen da ya zarga da bata masa suna da yada ƙarya a kansa.
Ya nuna cewa bayan sauraron jawabin limamin cocin a lokacin hudubar ibadar, ya fahimci cewa sakon da ake isarwa yana da alaka kai tsaye da halin da yake ciki, wanda hakan ya sa ya yanke shawarar janye dukkan shari’o’in da ya shigar.
A cikin hudubar da ya gabatar, babban limamin cocin kuma mataimakin shugaban limamai, Very Reverend Father Donatus Udoette, ya bukaci mabiya addinin su rungumi sulhu da yafiya, tare da barin abubuwan da suka faru a baya domin samun ci gaba da kwanciyar hankali.
Matakin da Akpabio ya dauka ya kawo karshen dukkan rigingimun shari’a da suka shafi zargin bata suna da aka yi ta yadawa a bainar jama’a, lamarin da ke nuna rufe wannan babi tun a farkon sabuwar shekara.
NAN













































