Tinubu ya yaba da kyawawan halayen Hadiza Bala Usman yayin cikar ta shekara 50 a duniya

WhatsApp Image 2026 01 02 at 02.02.00 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya taya mai ba shi shawara ta musamman kan daidaita manufofi kuma shugabar sashen daidaita sakamakon ayyukan gwamnati ta tsakiya murnar cikar ta shekara 50, wadda ta cika a ranar 2 ga Janairu, 2026.

Tinubu ya bayyana Hadiza Bala Usman a matsayin cikakkiyar ’yar ƙasa mai kishin kasa, yana mai cewa tsawon aikinta a hidimar jama’a ya kunshi sadaukarwa, jajircewa da himma wajen ci gaban kasa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya bayyana cewa kusan shekaru talatin da Hadiza ta shafe tana aikin gwamnati sun zama darussa masu ɗorewa na ƙwazo da shugabanci mai manufa.

Shugaban ƙasar ya tuno da farkon aikinta a hukumar kula da kamfanonin gwamnati, inda tun tana matashiya ta nuna hangen nesa mai zurfi da fahimtar sauye-sauyen tsarin da ake bukata domin bunkasa tattalin arziki.

Tinubu ya kuma jaddada rawar da ta taka a hukumar kula da kasuwanci ta birnin Abuja da kuma hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, yana mai cewa nasarorin da ta samu sun kafa muhimman alamomi ta fuskar karya shinge, ɗaga ƙa’idoji da karfafa gaskiya a harkokin gudanarwa.

Bugu da ƙari, shugaban ƙasar ya yaba da gudummawar siyasar da ta bayar, musamman a fannin gina jam’iyya da cibiyoyi a cikin APC, inda hakan ya taimaka wajen ƙarfafa tsari, inganci da ka’idojin dimokuradiyya, tare da cewa a matsayinta na shugabar sashen daidaita sakamakon ayyuka, ta ci gaba da nuna kwarewa da mayar da hankali kan sakamako da aiwatar da ajandar sabunta bege.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here