Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi zargin cewa manufar sauya fasalin naira na shugaban kasa Muhammadu Buhari na da nufin rusa dimokuradiyyar kasar nan.
Idan dai za a iya tunawa jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke gaban kotun koli da ke kalubalantar sahihancin manufar.
Zargin Ganduje ya zo ne sakamakon wahalhalun da ‘yan Najeriya ke shiga wajen samun sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000.
Shugaba Buhari a jawabin da ya yi ga ‘yan Najeriya a ranar Alhamis ya ce an musanya kudin Naira ne domin a daidaita hauhawar farashin kayayyaki da sauran matsalolin da suka shafi tattalin arziki.
A baya dai ba a san gwamnan Kano da fitowa ga-da-ga yana sukar shugaba Buhari ba kasancewar yana daya daga cikin mutanen da suka yi bakin kokarinsu wajen tallata shugaban ga masu zabe.
Ganduje ya bayyana hakane a lokacin da yake gana da kungiyar ‘yan majalisar dattawan shiyyar Arewa maso Yamma, da suka ziyarce shi domin su bayyana aniyarsu ta goyi bayan aniyar takarar shugaban kasa na Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.
Gwamnan ya ce abin takaici ne yadda duk da kokarin da jam’iyyar APC ta yi na tabbatar da nasarar Buhari a zabukan 2015 da 2019 bayan tafka asara da dama, shugaban ya kuduri aniyar biyan jam’iyyar da wadanda suka mara masa baya ta hanyar ruguza jam’iyyar da ta kai shi madafun iko.
“Mene ne dalilin yin hakan yanzu? Me ya sa bai yi haka ba a cikin shekaru bakwai da suka gabata? Menene ma’anar waɗannan dukka? Wannan gwamnan na CBN ba dan siyasa ba ne; bai san komai ba game da siyasa. Ta yaya dan siyasa zai ji dadin wannan siyasar? Ka yi tunanin yadda a matsayinka na jagora kake kallon bankunan da wuta ta cinye, idan ba wai dimokuradiyya ta ruguje ba, hakan zai yiwu?
“Kotun koli ta ce har yanzu tsofaffin takardun kudin suna kan doka, don haka duk bankin da ya ki karba, zan soke takardar shaidarsa,” inji shi.
F3anduje ya kuma bayyana cewa Tinubu zai janye manufar bayan zaben.













































