Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi watsi da zargin da gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi cewa shi ne ke haddasa tuhumar daukar nauyin ta’addanci da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi wa kwamishinan kudi na jihar Bauchi.
A ranar Laraba, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gurfanar da Yakubu Adamu, kwamishinan kudi na jihar Bauchi, kan zargin daukar nauyin ta’addanci da ya kai kimanin dalar Amurka miliyan 9.7.
Bayan gurfanar da kwamishinan, Bala Mohammed ya zargi gwamnatin tarayya da amfani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa wajen gallaza masa da mambobin majalisar gwamnatinsa saboda kin shiga jam’iyyar APC.
Da yake mayar da martani yayin ganawa da magoya bayansa a karamar hukumar Abua/Odual a jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana cewa gwamnan Bauchi yana danganta dukkan matsalolin da gwamnatinsa ke fuskanta da shi.
Labari mai alaƙa: Wike na yunkurin rusa ni ta hanyar amfani da hukumar EFCC wajen kai hari kan ƴan majalisa ta – Bala Mohammed
Ministan ya kuma zargi Bala Mohammed da kokarin kakaba shugabannin jam’iyya a jihar Rivers a lokacin da yake gwamna, yana mai cewa ya taba gargadin sa cewa hakan zai jawo rikici, abin da daga baya ya tabbata.
Nyesom Wike ya ce gwamnan Bauchi ya kamata ya dauki alhakin matsalolinsa na siyasa maimakon dora laifi a kansa, yana mai jaddada cewa ba shi da hannu a binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ke yi.
Ya kara da cewa idan gwamnan jihar Bauchi da gwamnatinsa ba su da laifi, ya dace su je su kare kansu a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa maimakon yada zarge-zarge, yana mai cewa ba daidai ba ne a dora masa alhakin kowace matsala da ta taso a fadin kasar nan.













































