Badakalar Naira Biliyan 20: Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta damke magatakardar babban kotu, da wasu lauyoyi

WhatsApp Image 2025 02 13 at 20.18.24 1 750x430

Hukumar karbar Korafe-korafen Jama’a da yaki da cin Hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kama wani magatakarda na babbar kotu da mataimakinsa Sheriff mai ritaya, da lauyoyi uku da wasu mutane 10 daga cikinsu jami’an tsaro da kuma mai bayar da beli bisa zarginsu da hannu a badakalar kudi sama da Naira biliyan 20.

SolaceBase ta ruwaito cewa shugaban PCACC, Muhuyi Magaji Rimin-Gado ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da ya kira a hedikwatar hukumar da ke Kano.

Shugaban Hukumar ya yi karin haske kan yadda ake tafka barna a Kano, inda ya bayyana cewa ana taimaka wa haramtattun ayyuka a matsayin manyan laifuka.

“Mun gano wata kungiyar masu aikata laifuka da suka kware wajen kwace filayen jama’a. Abin da ke da zafi shi ne hadin gwiwar wasu lauyoyi, ma’aikatan kotuna, jami’an rajistar filaye, da ma jami’an tsaro wajen aikata laifin,” inji shi.

Shugaban ya bayyana cewa an fallasa sirrin nasu ne bayan wata babbar kotun Kano ta bayar da umarnin kamawa tare da gudanar da bincike kan wani babban wanda ake zargi, Suleman Ali.

A cewar hukumar, an kama sama da mutane 15 da ake tuhuma da suka hada da lauyoyi uku da jami’ai hudu na ma’aikatar kasa da tsare-tsare, wasu daga cikin mutanen da aka kama suna hannun hukumar ne bayan umarnin da kotu ta bayar, yayin da wasu kuma aka bayar da belinsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here