Da yake bayyana sakamakon zaben, babban jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, ya ce Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, da ya doke babban abokin hamayyarsa, Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 890,705.
(Hoto: Abba Kabir Yusuf Facebook)