Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabiru Yusuf a halin yanzu yana kan gaba akan abokin hamayyarsa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC da tazarar kuri’u sama da dubu 81,000.
Daga sakamakon da Solacebase ta tattaro a cibiyar tattara sakamakon zaben jihar, Abba Kabir ya samu kuri’u dubu 911 da 374 yayin da Nasir Gawuna na jam’iyyar APC mai mulki ya samu kuri’u dubu 822 da 873, inda aka samu tazarar kuri’u dubu 88 da 501.












































